Ana Zaben Raba Gardama A Gabon

Kasar Gabon na gudanar da kuri’ar raba gardama domin amincewa da sabon kundin tsarin mulki, wanda ake gani a wani mataki na mayar da kasar

Kasar Gabon na gudanar da kuri’ar raba gardama domin amincewa da sabon kundin tsarin mulki, wanda ake gani a wani mataki na mayar da kasar tafarkin Dimokradiyya.

Shugaban mulkin sojin kasar Janar Brice Oligui Nguema – wanda ya kawo karshen mulkin iyalin gidan Bongo na tsawon gomman shekaru – ya alkawarta mayar da mulki zuwa farar hula cikin shekara biyu.

Masu goyon bayan sabon kundin tsarin mulkin sun bayyana matakin a matsayin wani mataki na sabunta makomar kasar, bayan tsawon shekara 50 na mulkin iyalan gidan Bongo.

Amma masu suka na cewa an tsara sabon kundin tsarin mulkin ta yadda zai taikama wa masu mulkin kasar, inda suke gargadin hakan ka iya haifar da mulkin mulaka’u.

Sabon kundin tsarin mulkin ya tanadar wa shugaban kasa wa’adin mulkin biyu na shekara bakwai-bakwai.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments