Jakadan Iran A Lebanon Ya Ce Tarwatsa Na’urar Sadarwar Hannu A Lebanon Laifin Yaki Ne

Jakadan Iran a Labanon ya jaddada cewa: Tarwatsa na’urar sadarwar hannu da ya faru a Lebanon laifi ne na yaki Jakadan Jamhuriyar Musulunci ta Iran

Jakadan Iran a Labanon ya jaddada cewa: Tarwatsa na’urar sadarwar hannu da ya faru a Lebanon laifi ne na yaki

Jakadan Jamhuriyar Musulunci ta Iran a kasar Lebanon Mujtaba Amani ya bayyana cewa: Benjamin Netanyahu fira ministan haramtacciyar kasar Isra’ila ya dauki alhakin aikin ta’addanci ta hanyar tarwatsa na’urar sadarwar hannu a cikin ‘yan kwanakin baya-bayan nan da suka gabata a kasar Lebanon, wanda ake kallo a matsayin laifin yaki.

A cikin wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin a yammacin jiya Talata, Amani ya ce: Kungiyar Hizbullah ta siyi na’urar ce, ba don yi amfani da su wajen aikin soja ba.

Dangane da zargin cewa; ‘Yan kungiyar Hizbullah ne kawai suke amfani da wannan na’urar sadawar, Amani ya ce: ‘Yan Hizbullah ba su taba yin amfani da wadannan na’urori wajen aikin soja ba. Wannan ikirarin karya ce, kuma amfani da ita a tsakanin fararen hula ya yadu sosai. Kuma ya ce shi ba soja ba ne, amma an ba shi wannan na’urar don sanarwar gaggawa.

Jakadan na kasar Iran ya jaddada cewa: Hatta a cikin wadanda suka yi shahada da wadanda suka jikkata a cikin wannan lamari akwai mata da kananan yara, wanda hakan ke nuni da cewa talakawa ma suna amfani da wadannan na’urori.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments