A daren jiya Talata sojojin Amurka sun kai hare-hare a yankuna mabanbanta na Syria da su ka hada da Bu-kamal, da hakan ya yi sanadiyyar shahadar mutane 3 da kuma jikkata wasu 4.
Wannan harin na Amurka dai ba shi ne na farko ba akan sansanoni mabanbanta na Syria a karkashin kare HKI da take yi ba tare da haddi ba.
Kwanaki uku da su ka gabata an kai hari akan wajen hako man fetur dake Deir-Zur” wanda Amurkan ta mamaye take kusa satar man dake wajen tana sayarwa da bai wa ‘yan ta’adda kudaden domin su yi amfani da su.
Cibiyar hako man fetur ta “al-Umar” ta fuskanci hari da makamai masu linzami daga ‘yan gwgawarmaya da zummar korar Amurkawa daga wajen.