Tsawon kwanaki dari hudu na yakin kisan gillar da ake yi a Gaza, adadin shahidai yana kara karuwa a cikin munanan laifukan kisan kare dangi kan al’ummar Gaza.
Babu wani wuri a Zirin Gaza da hare-haren bama-bamai ba su shafa ba, kamar yadda a halin yanzu ‘yan mamaya suka fi tsananta kai hare-haren kan arewacin Zirin Gaza, inda Falasdinawa mata da maza da kananan yara gami da tsofaffi suke fuskantar luguden wuta ba kakkautawa dare da rana.
Babu wani agajin jin kai da yake shiga yankin Zirin Gaza, domin duk mashigar da ake bi sojojin mamaya sun rufe su, kuma duniya ta zuba ido tana kallon yadda ake aiwatar da kashe-kashen rayukan bil’Adama da kone-konen gine-gine da kara watsuwar masifar yunwa da kishir runa da kuma hana samun magunguna ga marasa lafiya.
Alkaluman sun bayyana wani bangare na mummunan lamari cewa: Adadin Falasdinawan da suka yi shahada ya kusaci shahidai 45,000, wadanda 17,000 daga cikinsu yara ne, kuma 11,700 daga cikinsu mata ne. Wannan yana nufin kashi 72 cikin dari na wadanda suka yi shahadan yara ne da mata.
Kamar yadda kididdiga ta bayyana cewa: Adadin wadanda suka jikkata, ya zarce 102,000, kuma kashi saba’in da biyar cikin dari yara ne da mata, baya ga wadanda suka bace da suka haura mutane 10,000 da ake tunanin suna karkashin baraguzan gine-gine.