Mayakan kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah da ke kasar Lebanon sun kai wasu jerin hare-hare kan matsugunan yahudawa sahayoniyya ‘yan kaka gida na Kiryat Shimona da makamai masu linzami a safiyar yau Asabar.
A cikin wata sanarwa da kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah ta fitar ta bayyana cewa: Domin jaddada nuna goyon baya ga al’ummar Falastinu masu gwagwarmaya a Zirin Gaza da kuma goyon bayan gwagwarmaya da jajircewarta madaukakiya da kuma kare kasar Lebanon da al’ummarta, gami da gargadin da gwagwarmayar Musulunci ta Lebanon ke yi wa yahudawan sahayoniyya ‘yan kaka gida da suke matsugunan arewacin haramtacciyar kasar Isra’ila, Mujahidan kungiyar Hizbullah da safiyar yau Asabar sun yi luguden makamai masu linzami kan matsugunan da suke shiyar arewacin Isra’ila musamman matsugunin Kiryat Shimona.
Kamar yadda ‘yan gwagwarmayar kungiyar ta Hizbullahi suka kaddamar da hare-haren makamai masu linzami kan sansanin masana’antun soji na Zuvulon da ke arewacin birnin Haifa da misalin karfe 09:00 na safiyar yau Asabar.