Jakadan Sudan a Iran ya bayyana cewa: Al’ummar Sudan na maraba da karfafa alaka tsakanin Sudan da Iran
Jakadan Sudan a kasar Iran, Abdul-Aziz Hassan Saleh, ya jaddada cewa: Dangantakar dake tsakanin Sudan da Jamhuriyar Musulunci ta Iran na samun babban goyon baya daga shugabannin Sudan.
A hirarsa da gidan talabijin na Al-Alam na kasar Iran, jakadan kasar Sudan a Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya kara da cewa: Manufar harkokin wajen Sudan ta ginu ne kan hadin kai da rashin tsoma baki a cikin harkokin wasu kasashe, kuma al’ummar Sudan na maraba da karfafa dangantakar dake tsakanin kasarsu da Jamhuriyar Musulunci ta Iran.
Hassan Saleh ya ce: Yanzu haka suna cikin wani sabon tsari a Sudan kuma sun bude shafi mai tsafta don ciyar da wadannan alakoki gaba da kuma bunkasa su.
Saleh ya kara da cewa, al’ummar Sudan suna maraba da goyon baya gami taimakawa ci gaban wannan alaka a dukkan bangarori, kuma siyasar harkokin wajen Sudan ta ginu ce a kan manufofin taimakekkeniya da girmama manufofi tsakanin abokai da kuma rashin tsoma baki a cikin harkokin cikin gidan wata kasa, tare da jaddada kulla alaka bisa maslahar juna.