Sharhi : Zaben Amurka, wanda ya fi kowanne jawo rarrabuwar kawuna a tarihi

A ranar Talata, nan ce 5 ga wata, Amurkawa ke zaben shugabansu na 47. A fafatawar mai zafi, Mataimakiyar Shugaban Kasa Kamala Harris ta jam’iyyar

A ranar Talata, nan ce 5 ga wata, Amurkawa ke zaben shugabansu na 47.

A fafatawar mai zafi, Mataimakiyar Shugaban Kasa Kamala Harris ta jam’iyyar Democratic na fafatawa da tsohon shugaban kasar Donald Trump.

Sauran ‘yan takarar uku su ne mai fafutukar siyasa dan shekaru 39 Chase Oliver na jam’iyyar LP mai neman ‘yanci da Jill Stein mai shekaru 71 daga jam’iyyar GP, da dan takara mai zaman kansa mai shekaru 71, Cornel West.

Amma Harris mai shekaru 60 da Trump mai shekaru 78 ne manyan ‘yan takara.

Za’a fafata a zaben mafi daukan hankali a tsakanin ‘yar takara magajiyar Joe Biden daga jam’iyyar Demokrate da kuma tsohon shugaban kasar Donald Trump daga jam’iyyar Republican.

Idan har Trump, ya lashe zaben zai zama shugaban Amurka na biyu a tarihin kasar da ya lashe zaben shugaban kasa ba a jere ba, bayan Grover Cleveland a karshen karni na 19.

Idan Trump ya yi nasara kuma zai zamo shugaban ƙasa na farko da aka taɓa tuhuma da aikata manyan laifuka.

Ita kuwa ‘yar takara Harris tana neman zama mace ta farko, Ita kuwa Haris tana fatan zama mace ta farko, kuma mace baƙar fata ta farko, sannan ‘yar asalin yankin Asiya ta farko da za ta shiga Fadar White House.

A ranar Talata Jirage marasa matuƙa na ta shawagi a sararin samaniya sannan gwanayen harbi daga ɓoye suna ta sa ido a yayin da miliyoyin Amurkawa ke kaɗa ƙuri’unsu a zaɓen da ya fi kowanne jawo rarrabuwar kawuna a tarihi, wanda ke matuƙar jan hankali.

Jami’ai sun samar da matakan tsaro a rumfunan zabe a fadin ƙasar a ƙoƙarinsu na tabbatar da cewa komai ya gudana cikin aminci.

Don ƙara ƙarfafa tsaro, an girke ‘yan sanda da dama a kan tituna a faɗin ƙasar.

An ta rufe harkokin kasuwanci a yankunan da ke kusa da Fadar White House tare da ɗaukar matakan tsaro yayin da ake taka tsantsan cikin fargabar ɓarkewar rikici a ranar zaben – da kuma kwanaki masu zuwa.

Masu zaben dai a Amurka zasu yanke hukunci ne kan zaben da ka iya sa Kamala Harris ta zamo shugabar Amurka mace ta farko a tarihi ko kuma ya baiwa Donald Trump damar yin kome abin da kuma ke razana duniya.

A yayin da aka bude rumfunan zabe a fadin Amurka a ranar zabe, ‘yar takarar jam’iyyar Democrat mataimakiyar shugaban kasa Kamala Harris, mai shekaru 60 da dan takarar jam’iyyar Republican tsohon shugaban kasa Donald Trump, mai shekaru 78, sun yi kankankan a takarar shugaban Amurka mafi rashin tabbas a zamanin da muke ciki.

Abokan hamayyar sun shafe ranaikun karshe na yankin neman zabensu suna kokarin yiwa magoya bayansu kaimi domin su fito suyi zabe tare da kokarin shawo kan duk mai niyar zaben da bai yanke dan takarar da zai zaba ba a jihohin rabagardamar da ake sa ran zasu sauya alkaluman zaben.

Za’a shafe kwanaki kafin sanin sakamakon karshe idan har aka yi kankankan kamar yadda zaben ke nunawa, inda yake kara zaman dardar a kasar dake fama da rabuwar kannu.

A 2020 Trump ya ƙi yarda da shan kaye kuma ya angiza magoya bayansa suka kai farmaki suka mamaye majalisa, lokacin da majalisar ke taro domin tabbatar da nasarar joe Biden.

Zaben na ban aya zo ne a daidai lokacin da siyasar duniya  ta yi tsami  dangane da yakin Ukraine da na Gabas ta Tsakiya.

Gwamnatin Amurka ƙarƙashin shugaba Biden da Harris, tana bai wa Ukraine goyon baya mara iyaka, yayin da a Gabas ta Tsakiya, suka yi watsi da ta’asar da Isra’ila ke yi wa Falasɗinawa da kuma hare-hare a Lebanon.

Goyan bayan da gwamnatin Amurka ke baiwa Isra’ila kan duk wata irin ta’asa da take aikatawa ba wai wani abu ne da wanda aka zama zai sauya ba.

A cewar wani rahoto a baya-bayan nan da Cibiyar Watson mai kula da harkokin kasa da kasa da al’amuran jama’a ta Jami’ar Brown ta yi, Biden da Harris sun ba da taimakon dala biliyan 17.9 ga Isra’ila tun daga ranar 7 ga Oktoba, 2023.

Gwamnatin Amurka karkashin Biden da Harris, ta bai wa gwamnatin Isra’ila makamai masu guba da aka yi amfani da su wajen kashe fararen hula a Gaza da Lebanon tare da lalata ababen more rayuwa.

A gefe guda kuma, Donald Trump, wanda aka sani da kusanci sosai da gwamnatin Isra’ila, musamman a lokacin mulkinsa na baya daga 2017 zuwa 2021 kuma.

A wani taro a ranar 7 ga Oktoba, 2024—yayin cika shekara guda da fara yaƙin Gaza, Trump ya bayyana kansa a matsayin mala’ika mai kare gwamnatin Tel Aviv.

A cikin gida Amurka, al’ummar bakar fata ba za su manta da tarihin gwagwarmayar da suka yi wajen sauya tsarin mulki don samun ‘yancin yin zabe ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments