An Yi Ba- Ta- Kashi A Tsakanin ‘Yan Gwagwarmaya A Gaza Da Sojojin Mamaya

 Dakarun rundunar “Kassam” na kungiyar Hamas sun sanar da kai jerin hare-hare akan sojojin mamayar HKI a yau Talata a arewacin Gaza. Sanrwar ta ce

 Dakarun rundunar “Kassam” na kungiyar Hamas sun sanar da kai jerin hare-hare akan sojojin mamayar HKI a yau Talata a arewacin Gaza.

Sanrwar ta ce mujahidai sun yi nasarar kai hari akan sojojin kasa na ‘yan mamaya su 5 daga kusa, ta hanyar amfani da manyan bindigoi da kuma bama-bamai akan titin “Al-Hujah’ dake tsakiyar sansanin Jabaliya a arewacin Gaza.

 Bugu da kari, dakarun na “Kassam” sun yi amfani da makamin “Yasin101” akan wata tankar yaki samfurin “Mirkava” a kusa da asibitin “Yamanussa’id” a tsakiyar sansanin Jabaliya.

A cikin Gaza dakarun na “Kassam” sun yi fada gaba da gaba da sojojin mamaya a yau Talata.

 Ita kuwa rundunar “Alwiyatul-Salahuddin’ tare da hadin gwiwar rundunar “Shahid Umar Kassim” sun kai harin akan  ayarin motocin yaki na ‘yan mamaya a arewa maso yammacin Beit Lahiya dake arewacin Gaza.

Amma rundunar “Kata’ibu Shuhadaul-Aqsa” ta sanar da kai wani harin akan motocin yaki na ‘yan sahayoniya akan titin Rashid a yankin “Nastarim” .

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments