Wani sojan bayahauden Isra’ila ya kashe kansa bayan an kira shi zuwa aiki, a cewar kafafen yada labarai na haramtacciyar kasar Isra’ila.
Hukumar yada labaran Isra’ila ta watsa rahoton a wannan Litinin, amma ba ta ambaci sunan sojan ba.
Lamarin ya faru ne kasa da mako guda bayan da kafafen yada labarai na Isra’ila suka bayar da rahoton mutuwar wani fitaccen dan ta’adda cikin sojojin Isra’ila mai suna Asaf, wanda ya kashe kansa tun da farko bayan ya fito da sunan zai yi kiran waya.
A watan da ya gabata, mahaifiyar wani sojan Isra’ila da ya kashe kansa ta shaida wa CNN cewa, abin da ya gani a Gaza kadai na iya sanya shi ya kashe kansa.
A cewar mahaifiyar tasa, Eliran Mizrahi ya dawo a matsayin wani mutum na daban, wanda ya samu raunuka a yakin Gaza, kuma sau da yawa yana kwatanta abin da ya gani da cewa baya faduwa saboda muninsa.
Dubban sojoji ne ke fama da matsalar damuwa bayan tashin hankali ko kuma matsalolin lafiyar kwakwalwa, sakamakon abubuwan da suka faru da su ko kuma suka aikata a Gaza.
Hukumar ta IOF ba ta bayar da adadin sojojin da suka kashe kansu ba, amma wani likita ya shaida wa CNN a boye cewa, da yawa daga cikin sojojin Isra’ila ba su amince da kudirin gwamnati ba.