Ministan Harkokin Wajen Kasar Iran Ya Ce Iran Ta Sha Yin Gargadi Ga ‘Yan Sahayoniyya

Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Iran ta sha gargadin ‘yan sahayoniyya da kada su gwada nufin Iran Ministan harkokin wajen kasar Iran

Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Iran ta sha gargadin ‘yan sahayoniyya da kada su gwada nufin Iran

Ministan harkokin wajen kasar Iran Sayyid Abbas Araqchi ya ce: Ya sha maimaita sakon da suka aike wa yahudawan sahayoniyya a ziyarar da ya gudanar a kasashen yankin Gabas ta Tsakiya, kuma wannan sakon ya yi gargadin kada su gwada matsayin Iran, saboda Iran ta shige matsayin gwaji, ya kuma bayyana cewa Iran ba ta daukan zaben shugaban kasar Amurka da wata kima ta a zo a gani, yana mai jaddada cewa wadannan zabukan ba su da wani tasiri a kan matsayar Iran.

Wannan dai ya zo ne a wata hira da tashar talabijin ta Iran ta 1 ta yi da ministan harkokin wajen kasar Abbas Araqchi, wadda aka watsa da yammacin jiya Litinin a daidai lokacin da ake juyayin cika kwanaki arba’in da shahadar Sayyed Hassan Nasrallah, tsohon babban sakataren kungiyar Hizbullah.

Araqchi ya ce: Harin daukan fans ana “Alkawarin Gaskiya na 2” wani aiki ne na kariya gaba daya kan zaluncin da ake yi al’umma, bisa dogaro da hakkin kare kai da dokokin kasa da kasa, da kuma Yarjejeniya ta Majalisar Dinkin Duniya suka tanada.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments