Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Kasar Iran tana amfani da dukkan karfi ne wajen mayar da martani ga harin ‘yan sahayoniyya
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i ya jaddada cewa: Goyon bayan ikon kasa da kuma ‘yancin fadin kasar, wata manufa ce ta asali, kuma tsarin mayar da martani ga hare-haren ‘yan sahayoniyya a bayyane yake, kuma a lokaci guda, abu ne da ya dace ga Iran ta yi amfani da dukkanin karfinta wajen mayar da martani ga waɗannan hare-haren wuce gona da iri.
A cikin taron manema labarai na mako-mako a jiya litinin, Baqa’i ya ce: Taimakawa ‘yancin kan kasa da kuma tabbatar da amincin kasar wani tsari ne na tushe, kuma wani abu ne da mahukuntan Iran suka tabbatar a aikace, kuma yanayin martanin da suka tsara kan hare-haren ‘yan sahayoniyya a bayyane suke. kuma a lokaci guda abu ne na dabi’a cewa su yi amfani da duk damar kayan aiki da dabi’u don mayar da martanin kan wadannan hare-hare.
Kakakin ya kara da cewa: Matsayin Iran a hukumance a fili yake wajen kin mallakar makaman kare dangi da kuma tabbatar da Shirin zaman lafiya na makamashin nukiliyarta, sannan a lokaci guda kuma kamar yadda Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ce, Iran za ta kasance cikin dukkan shiri da ya dace don kare kan Iran.