Jami’in Kungiyar Hamas Ya Jaddada Bukatar Hukunta Gwamnatin ‘Yan Sahayoniyya

Babban jami’in kungiyar Hamas ya jaddada cewa: Dole ne kasashen duniya su matsa kaimi wajen hukunta ‘yan sahayoniyya tare da mayar da su saniyar ware

Babban jami’in kungiyar Hamas ya jaddada cewa: Dole ne kasashen duniya su matsa kaimi wajen hukunta ‘yan sahayoniyya tare da mayar da su saniyar ware a duniya

Jagora a kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas Osama Hamdan ya bayyana cewa: Dole ne gwamnatin Amurka mai ci ta daina goyon bayan ‘yan mamaya, ta koma ga kokarin kwato hakkin al’ummar Falastinu da ake zalunta, saboda gwamnatin Amurka da ta gabata da ta yanzu duk suna da hannu a aiwatar da laifukan ta’asa kan al’ummar Falasdinu.

A taron manema labarai da ya gudanar a jiya Litinin, Hamdan ya kara da cewa: Dole ne kasashen duniya su dauki matakin hukunta gwamnatin ‘yan sahayoniyya da mayar da ita saniyar ware, da kuma korarta daga dukkanin cibiyoyin Majalisar Dinkin Duniya, lamarin da ke nuni da cewa yakin da ‘yan mamaya suke yi kan asibitoci, aiwatar da kisan kare dangi da kuma keta yarjejeniyar kasa da kasa. yayin da Falasdinawa sama da 100,000 a arewacin Gaza sun rasa duk wani abin bukatar rayuwa. A fili yake cewa: Gwamnatin Amurka da al’ummomin duniya ne ke da alhakin wadannan laifuka.

Osama Hamdan ya jaddada cewa ta’addancin yahudawan sahayoniyya da Amurka ke marawa baya, duk yadda ya kasance ba zai taba rusa lagon ‘yan gwagwarmaya da suke neman hakkokinsu ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments