Hukumar FA ta Ingila ta ba da Hakuri ga wata ‘yar wasa musulma mai sanye da lullubi

Hukumar kwallon kafa ta Ingila (FA) ta bayar da hakuri ga wata yar wasan kwallon kafa ta kasar kan yin mu’amala da ita ta hanyar

Hukumar kwallon kafa ta Ingila (FA) ta bayar da hakuri ga wata yar wasan kwallon kafa ta kasar kan yin mu’amala da ita ta hanyar da ba ta dace ba saboda ta sanya lullubi.

An hana ‘yar wasan kwallon kafa musulma, Iqra Ismail, daga buga wasan Greater London Women’s Football League (GLWFL) saboda sanya riga da dogon wando maimakon gajeren wando, saboda akidar ta.

Ismail, mai shekaru 24, tsohuwar kyaftin din tawagar ‘yan wasan kasar Somaliya kuma mai ba da shawara ga mata musulmi a fagen wasanni, tana shirin shiga filin wasan a matsayin wadda za ta maye gurbin wata ‘yar wasa a was an United Dragons FC. Sai dai kafin shigowarta, alkalin wasan ya sanar da ita cewa ba za ta iya shiga ba sai dai idan ta bi ka’idojin gasar.

 A cikin bacin rai, Ismail ta bayyana cewa ta sanya rigar wando don bin imaninta tsawon shekaru biyar da ta yi tana buga wasa a wannan gasar ba tare da wata matsala ba. Ismail ta ce: “Na ji an mayar da ni saniyar ware sosai da aka ce ba zan iya wasa ba saboda imanina.

A martanin da FA ta mayar, ta bayar da uzuri cikin gaggawa, inda ta jaddada kudurinta na hada kai tare da tabbatar da cewa ya kamata a ba ‘yan wasa damar sanya tufafin da suke mutunta addininsu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments