Sheikh Na’im Kassim wanda ya gabatar da jawabi na farko a jiya Laraba bayan da aka zabe shi a matsayin Sabon sakataren kungiyar gwgawarmaya ta Hizbullah, ya sha alwashin cigaba da ayyukan Shahid Sayyid Hassan Nasrallah, tare da jaddada cewa za su yi nasara a fadan da suke yi da HKI.
Sheikh Na’im Kassim ya kuma ce; Gwgawarmaya tana da karfin da za ta iya dakile manufar Isra’ila da kuma Amurka, sannan kuma a karshe ta yi nasara.
Sheikh Na’im Kassim ya kuma ce, Ba su son yaki, amma sun riga sun shirya yinsa idan aka kallafa musu shi, kuma za su yi nasara, sannan kamar yadda shugabanmu shahid sayyid ya ambata,muna sauraron abokan gama domin kwamawa da su.
Sabon shugaban kungiyar ta Hizbullah ya yi ishara da harin da Isra’ila ta kai wa ma’aikatan kungiyar ta hanyar sadarwa ta “Pager” da kuma kashe jagororin gwawarmaya da ta yi, da su ka hada da Shahid Sayyid Hassan Nasarallah, duk sun yi tasiri akan kungiyar Hizbullah, amma ta shanye wannan bugun, ta kuma cigaba da tsayin daka a filin daga.
Sheikh Na’im Kassim ya kuma ce; Abinda yake faruwa a filin daga ya tabbatar da cewa kungiyar ta girgije domin ta ginu ne akan cibiyoyi kuma tana da kayan aiki masu yawa.