A wani rahoto da tashar talbijin din ‘almanar’ ta wallafa ta bayyana cewa; sojojin mamayar sun fice daga garuruwan Hula, Markaba, Meis-jabal, Balida da kuma Udaisha.
Rahoton ya kara da cewa, sojojin mamayar sun janye motocinsu na yaki daga wasu garuruwan da su ka shiga, su ka koma can cikin Falasdinu dake karkashin mamaya.
Jiragen sama marasa matuki na ‘yan gwagwarmaya sun yi shawagi a samaniyar iyakar Lebanon inda su ka tabbatar da janyewar sojojin mamayar.
Janyewar sojojin mamayar dai yana da alaka ne da tsoron da suke da shi na ‘yan gwgagwarmaya, bayan da su ka kai musu hare-hare da kashe da dama daga cikinsu.
Tun daga shigar sojojin na HKI a wasu yankuna na iyakar Lebanon, babu ranar da ba a kashe su da jikkata su.
A jiya Litinin mayakan Hizbullah sun sanar da cewa a cikin wata guda daga kutsen ‘yan mamaya, sun kashe sojoji 90 da kuma jikkata wasu 750. Haka nan kuma sun lalata tankokin yaki samfurin “Mirkava’ 38 da buldoza 4, sai motar jigilar sojoji daya. Haka nan kuma sun harbo jirgi maras matuki samfurin Hermers 450 guda 3 da kuma guda daya Hermers 900 guda daya.