Sojojin Isra’ila sun kashe akalla mutane 53 a Gaza da kuma wasu 21 a Lebanon a ranar Lahadi, yayin da babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bayyana kaduwarsa kan “mummunan yanayin da ake ciki.
Hare-haren Isra’ila sun kashe akalla mutane 21 a kudancin kasar Lebanon, a cewar ma’aikatar lafiya ta Lebanon.
Akalla mutane 9 ne suka mutu sannan wasu 38 suka jikkata a wani harin da aka kai kan Haret Saida, kusa da birnin Sidon mai tashar jiragen ruwa, in ji ma’aikatar a ranar Lahadi.
Ma’aikatar lafiya ta kasar Lebanon ta ba da rahoton mutuwar mutane 2,464 a kasar, yayin da a kalla 11,530 suka jikkata tun daga watan Oktoban 2023.
A Falasdinu kuwa akalla Falasdinawa 42,924, akasarinsu fararen hula aka kashe a zirin Gaza, a cewar ma’aikatar lafiya ta gwamnatin Hamas.
A halin da ake ciki dai an ci gaba da sabuwar tattaunawa a wannan Lahadin a birnin Doha tsakanin Isra’ila da Amurka da kuma Qatar domin tattauna tsagaita wuta a Gaza da nufin sako Isra’ilawan da aka yi garkuwa da su a ranar 7 ga watan Oktoban 2023.