Kafofin yada labaran yahudawan sahayoniyya sun watsa rahoton cewa: An kai wani hari da ya yi sanadiyyar halakar sojojin yahudawan sahayoniyya shida tare da jikkatan wasu kusan 50, ciki har da wadanda suke cikin halin rai kyaikyai mutu kyaikyai a kusa da hedkwatar hukumar leken asirin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila da ke arewacin birnin Tel Aviv ta Mossad.
Rundunar ‘yan sandan gwamnatin mamaya ta tabbatar da shahadar wanda ya kai harin da aka kai a kusa da hedkwatar hukumar leken asirin haramtacciyar kasar Isra’ila ta Mossad da ke mahadar Glilot a shiyar arewacin birnin Tel Aviv, kuma ta yi ikirarin cewa dan gwagwarmaya ne ya kai harin.
Wata kafar yada labaran Isra’ila ta bayyana cewa: Wanda ya kai harin a Glilot shi ne Rami Natour daga kauyen Qalanswa cikin yankunan Falasdinawa da aka mamaye.