Mai magana da yawun gwamnatin Iran Fatemeh Mohajerani ta jinjina wa dakarun tsaron saman kasar saboda irin matakan da suka dauka na kare wuraren soji daga hare-haren da Isra’ila ta kai a wannan Asabar, tana mai cewa matakin ya farfado da martabar al’ummar Iran.
Al’ummar Iran na alfahari da karfin tsaron kasarsu kuma sun gamsu da hakan, in ji Mohajerani a ranar Asabar.
Da take tsokaci a hukumance dangane da hare-haren da Isra’ila ke babatun cewa ta kaiwa Iran, kakakin ta ce an samu barna kadan ne kawai, tana mai kira ga jama’a da kada su kula da jita-jita da hotunan karya da “wasu kafafen yada labarai ke yadawa” da kuma bin diddigin labarai ta kafafen yada labarai masu Magana a hukumance.
Ta ce Iran na da karfi kuma irin wadannan munanan ayyukan ba za su iya haifar mata da matsala ba, ta kara da cewa a halin yanzu kasar na cikin yanayi na yau da kullum, komai yana tafiya ba tare da wani tsaiko ba, an ci gaba da gudanar da zirga-zirgar jiragen sama kamar yadda aka saba.
A safiyar wannan Asabar ne ofishin hulda da jama’a na rundunar tsaron sararin samaniyar kasar Iran ya fitar da sanarwa, inda ya sanar da cewa, an dakile hare-haren da jiragen yakin haramtacciyar kasar Isra’ila suka kai kan cibiyoyin soji a birnin Tehran, da lardin Ilam da ke yammacin kasar, da kuma lardin Khuzestan da ke kudu maso yammacin kasar, tare da yin nasara a kan makiya.