Rahotanni daga filin dagar kudancin Lebanon sun ambaci cewa, mayakan kungiyar Hizbullah sun rusa tankokin yakin HKI 5 a herin hare-hren da su ka kai musu a jiya Juma’a.
Bayanin da kungiyar ta Hizbullah ta fitar ya ambaci cewa, harin nasu ya yi sanadiyyar kashe da kuma jikkata sojojin da suke cikin tankokin yakin.
Harin farko da mayakan na Hizbullah ta kai ya kasance ne a kusa da garin Addisah, da misalin karfe 5:00 na yamma.
A kusa da garin Maskfaam, mayakan na Hizbullah sun yi nasarar rusa wasu tankokin yakin tare da kashe sojojin da suke cikinsu da jikkata wasu.
A tsakanin Misra da Addisah, mayakan na Hizbullah sun lalata wata tankar ta Mirkava tare da kashe sojojin da suke cikinta da kuma jikkata wasu da dama.
Sai kuma a garin Hola da shi ma mayakan na Hizbullah su ka rusa wata tankar ta Mirkava.
Agefe daya, a jiya Juma’a din kafafen watsa labarun HKI sun ambaci cewa, hare-haren da Hizbullah ta kai a jiya su ne mafi tsakanin tun da aka fara yaki.
A jiya Juma’a ne dai HKI ta sanar da cewa a cikin sa’oi 24 an kashe mata sojoji 10 a kudancin Lebanon.