Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah ta sanar da cewa: ‘Yan gwagwarmaya sun janyo gagarumar hasara ga makiya ta hanyar halaka sojoji 70 tare da jikkata wasu 600 na daban
Majiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah da ke kasar Lebanon ta fitar da takaitaccen bayani kan ayyukan jihadi da mujahidai suka aiwatar da ke tabbatar da cewa: ‘Yan gwagwarmaya sun janyo gagarumar hasara ga makiya yahudawan sahayoniyya ta hanyar halaka sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila fiye da 70 da kuma jikkata sama da 600 da suka hada da hafsoshi da sojoji, yayin da majiyoyin ‘yan mamaya suka yi furuci da halakar sojoji 4 kacal tare da jikkata wasu 15 sakamakon fashewar nakiya a kan hanyarsu a kudancin kasar Lebanon.
A ci gaba da kalubalantar hare-haren wuce gona da iri da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ke kaiwa kan kasar Lebanon, ‘yan gwagwarmayar kungiyar Hizbullah sun janyo wata gagarumar hasara ga sojojin makiya ta fuskar kayan aiki da halaka jami’ai da sojoji da dama, a fagen daga ta hanyar gudanar da gumurzu gaba da gaba har zuwa wuraren da suke karkashin mamayarsu da ke kasar Falasdinu da suka mamaye.