Shugaban Kasar Turkiyya Ya Bukaci Kakaba Takunkumi Kan Haramtacciyar Kasar Isra’ila

Shugaban kasar Turkiyya ya yi kira ga Majalisar Dinkin Duniya da ta kakaba wa haramtacciyar kasar Isra’ila takunkumin hana sayen makamai Shugaban kasar Turkiyya Rajab

Shugaban kasar Turkiyya ya yi kira ga Majalisar Dinkin Duniya da ta kakaba wa haramtacciyar kasar Isra’ila takunkumin hana sayen makamai

Shugaban kasar Turkiyya Rajab Tayyib Erdogan ya yi kira ga Majalisar Dinkin Duniya da ta dauki matakin kakaba takunkumin hana sayan makamai kan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila, yana mai la’akari da cewa: Wannan mataki ya kasance “mafi inganci” da zai kawo karshen yakin kisan kare dangi a Zirin Gaza.

Bayanin na Erdogan ya zo ne a cikin wata sanarwa da ya fitar bayan ganawar da ta dauki tsawon sa’o’i da yawa a Istanbul tare da ministocin harkokin wajen kasashen Rasha, Iran, Armeniya da Azabaijan.

Erdogan ya ce, Gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila tana neman tayar da hankali ne domin kara janyo tashe-tashen hankula a yankin, kuma ya yi la’akari da cewa; Kakaba takunkumin hana sayan makamai da Majalisar Dinkin Duniya za ta kakaba kan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila za ta zama wata hanya mai inganci don kawo karshen ta’addancin yahudawan sahayoniyya, wanda ya bayyana gwamnatin ‘yan mamayar a matsayar mai cin zarafin dokokin kasa da kasa.

Shugaban na Turkiyya ya yi nuni da cewa: Kasarsa za ta ci gaba da yin kira da a dauki wannan mataki na haramcin a dukkanin bangarorin kasa da kasa, yana mai jaddada cewa duk ranar da za ta wuce ba tare da tsagaita bude wuta ba, na kara fuskantar barazanar barkewar yaki a yankin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments