Hizbullah ta halaka sojojin Isra’ila 55 tare da jikkata sama da 500

Dakarun kungiyar gwagwarmayar musulunci ta Hizbullah sun kaddamar da munanen hare-hare da makamai masu linzami a kan sojojin Haramtacciyar kasar Isra’ila a sansanoninsu daban-daban da

Dakarun kungiyar gwagwarmayar musulunci ta Hizbullah sun kaddamar da munanen hare-hare da makamai masu linzami a kan sojojin Haramtacciyar kasar Isra’ila a sansanoninsu daban-daban da ke arewacin Falastinu da yahudawa suka mamaye.

Wannan yana zuwa ne a daidai lokacin da kungiyar take dakile yunkurin sojojin yahudawa na kutsawa kudancin Lebanon, inda tsawon makonni uku a jere ake kazamin artabu tsakanin darun Hizbullah da kuma na yahudawan Isra’ila.

Da misalin karfe 23:48 na daren jiya mayakan Hizbullah sun kai hari a sansanin ‘Filon’ da ke Rosh Pina a gabashin birnin Safad da yahudawa suka mamaye, tare da harba makami mai linzami, “a matsayin mayar da martani ga hare-haren da sojojin Isra’ila suka kai kan kauyukan kudancin Lebanon da kuma gidajen jama’a fararen hula.

Kafin wannan lokacin a ranar Alhamis da ta gabata, Hizbullah ta sanar da cewa, tun daga ranar da sojojin yahudawan Haramtacciyar Kasar Isra’ila suka fara yunkurin kutsawa cikin Lebanon zuwa a cikin kasa da makonni uku, Dakarun Hizbullah sun aike da sojojin Isra’ila 55 zuwa lahira, tare da jikkata wasu fiye da 500, da kuma ragargaza tankokin yaki sama da 20 da kuma wasu motocin daukar soji da na buldoza, wanann na zuwa ne a daidai lokacin da Isra’ila tana kokarin boye irin asarorin da sojojinta suke fuskanta  akarawarsu da dakarun Hizbullah.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments