Pezeshkian: Nauyi ne kan musulmi su dauki matakin dakile zaluncin gwamnatin sahyoniya

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya ce karin matsin lamba kan masu goyon bayan gwamnatin sahyoniyawan na iya dakatar da ayyukanta na kidan kiyashi. A

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya ce karin matsin lamba kan masu goyon bayan gwamnatin sahyoniyawan na iya dakatar da ayyukanta na kidan kiyashi.

A wata tattaunawa ta wayar tarho da shugaban kasar Oman Sultan Haitham bin Tariq Al Said a wannan Laraba, shugaba Pezeshkian ya godewa Muscat kan matakin da ta dauka kan take hakkin bil adama da Isra’ila ke yi  a Gaza da Lebanon, inda ya bukaci a kara hadin kai tsakanin kasashen musulmi.

“Idan kasashen musulmi suka yi aiki a matsayin daya, gwamnatin Sahayoniya ba za ta kuskura ta aikata ta’addanci cikin sauki ba, haka nan Amurka da kasashen yammacin duniya ba za su iya ba da goyon baya ayyukan ta’addancin Isra’ila ba,” in ji shi.

Pezeshkian ya kuma jaddada aniyar Tehran na karfafa alakar da ke tsakanin Tehra da Muscat, yana mai cewa dangantakar da ke tsakaninsu  na daga cikin muhimman batutuwan da Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta sa a gaba, kuma tana cikin tsarin fadada hadin gwiwa da kasashe makwabta.

A nasa bangaren, Sultan bin Tariq ya yaba da matsayin Iran kan batutuwan da suka shafi yankin da suka hada da Gaza da Lebanon, sannan ya jaddada bukatar kasashen yammacin Turai su kaucewa daukar matakai masu harshen damo wajen tunkarar irin wadannan matsaloli.

Har ila yau, ya jaddada cewa goyon bayan hakkin al’ummar Gaza da Lebanon da ake zalunta ya kasance wani muhimmin abu ga kasar Oman, yana mai cewa: Oman a kodayaushe na ci gaba da kalubalantar irin goyon bayan da kasashen yammacin duniya ke  baiwa laifukan Isra’ila, kuma hakan ba abu ne da za a amince da shi ba kowace fuska.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments