Babban Kwamandan Juyin Juya Halin Musulunci Na Iran Ya Ce: A Shirye Suke Su Kalubalanci Isra’ila

Dakarun kare juyin juya halin Musulunci za su kalubalanci duk wani mummunan yunkuri na makiya ‘yan sahayoniyya Babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci

Dakarun kare juyin juya halin Musulunci za su kalubalanci duk wani mummunan yunkuri na makiya ‘yan sahayoniyya

Babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran Manjo Janar Hossein Salami ya jaddada cewa: Iran za ta fuskanci duk wani mummunan yunkuri na makiya ‘yan mamayar yahudawan sahayoniyya da cikakken karfi da jajurcewa.

Manjo Janar Salami a sakonsa na taya murna ga Birgediya Janar Haji-zadeh kwamandan rundunar sojin sama ta dakarun kare juyin juya halin Musulunci a yayin bikin karrama shi da lambar yabo da jagoran juyin juya halin Musulunci ya yi: Yana cewa; Za su kara tabbatar wa al’ummar Iran cewa suna cikin gagaruman shirye-shiryen mayar da martani kan  makiya da kare kasa.

Ya kara da cewa: Sun jajirce kan dabarun jagoranci mai hikima na rashin sakaci da rashin gaggawar mayar da martani ga yunkurin makiya.

Sannan ya yi nuni da cewa: Za su ci gaba da ba da goyon baya ga bangaren gwagwarmaya, musamman a kasashen Lebanon da Falastinu, ya kuma ce: Aiki na hakika na 2 ya kasance wani abin da zai kawo sauyi ne wajen karfafa karfinmu na mayar da martani, wanda zai zama wani sauyi a kan tafarkin karfin iko da kariyar Iran, musamman a fagen harba makamai masu linzami.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments