Jaridar Yedioth Ahronoth ta haramtacciyar kasar Isra’ila ta nakalto daga majiya mai tushe cewa: Gwamnatin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila na shirin tunkarar kungiyoyin gwagwarmayar Musulunci a kasar Iraki, bayan da aka kashe sojojin yahudawa biyu tare da jikkata wasu ta hanyar kai hari da wani jirgin sama maras matuki ciki a yankin Tuddan Julan na kasar Siriya da aka mamaye.
Majiyoyin haramtacciyar kasar Isra’ila sun nakalto daga fira ministan haramtacciyar kasar Isra’ila cewa: Za su duba martanin da ya dace, ko da kuwa ta hanyar kai harin ne da jirgin sama maras matuki ciki domin mayar da martani kan kashe sojojinsu a Tuddan Julan.
Bangarorin Iraki da suka hada da dakarun Hizbullah, Bangaren sojin Sayyidul-Shuhada, da Harkar Nujaba, su ne suka kafa gwagwarmayar Musulunci a kasar Iraki.
A cikin ‘yan watannin da suka gabata, wadannan tawaga na ‘yan gwagwarmaya sun sanar da kaddamar da hare-haren jiragen sama marasa matuka ciki kan yankunan Falasdinu da aka mamaye domin nuna goyon baya ga gwagwarmayar Falasdinawa da kuma goyon bayan al’ummar Gaza.