Shugaban Iran Na Gudanar Da Ziyarar Aiki A Kasar Qatar

Shugaban kaar Iran masuod Pezeshkian ya fara gudanar da wata ziyarar aiki a kasar Qatar a wannan Laraba. Kamfanin dillancin IRNA ya bayar da rahoton

Shugaban kaar Iran masuod Pezeshkian ya fara gudanar da wata ziyarar aiki a kasar Qatar a wannan Laraba.

Kamfanin dillancin IRNA ya bayar da rahoton cewa, sarkin Qatar Sheikh Tamim bin Hamad Al Thani, ya tarbi shugaba Pezeshkian a fadar masarautar Qatar da ke Doha a yammacin wanann Laraba.

A wajen bikin maraba da aka yi wa shugaban na Iran a hukumance, an gabatar da wakilan manyan tawagogin kasashen biyu ga juna.

Manyan tawagogin kasashen biyu za su yi shawarwari a tsakaninsu, sannan shugabannin kasashen biyu za su gana da juna a kebe.

Haka nan kuma manyan jami’an kasashen Iran da Qatar za su rattaba hannu kan muhimman takardu na hadin gwiwa tsakanin Jamhuriyar Musulunci ta Iran da Qatar tare da halartar shugaban Iran da kuma sarkin kasar ta Qatar, sannan kuma zasu bayyana muhimamn abubuwan da aka cimmawa a ziyarar a taron manema labarai.

Qatar na daga cikin kasashen yankin gabas ta tsakiya da ked a kyakkayawar alaka da kasar Iran a dukkanin bangarori, na siyasa tattalin arziki cinikayya da kuma harkokin ilimi da tsaro.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments