Dangane da harin makami mai linzami da Iran ta kai kan gwamnatin Haramtacciyar Kasar Isra’ila, shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya yi gargadi da kashedi ga Netanyahu da cewa: ya kamata Netanyahu ya sani cewa Iran bat a neman yaki da kowa, amma ta tsaya tsayin daka wajen fuskantar kowace barazana, kuma wanan abin da aka gani wani bangaren kadan daga karfinmu, Kada ku shiga rikici da Iran.” In ji Pezeshkian.
Shugaban kasar ta Iran ya rubuta a shafinsa na dandalin sada zumunta na X dangane da harin makami mai linzami da Iran ta kai wa gwamnatin sahyoniyawa cewa:
Bisa la’akari da halastaccen hakki da kuma manufar samar da zaman lafiya da tsaro ga Iran da ma yankin, an mayar da martani mai ma’ana kan wuce gona da iri na gwamnatin Haramtacciyar Kasar Isra’ila.
Wannan matakin ya kasance domin kare muradu da al’ummar Iran daga barazana ta masu girman kai da zubar da jinin bil adama.
Saboda haka yana da kyau Netanyahu ya ya farka daga mafarkinsa, ya fuskanci hakika, idan kuma ya zabi yin fito na fito da kasar Iran, to ga fili ga mai doki, in ji shugaban na Iran.