Najeriya: Turji Ya Nemi Sulhu Da Gwamnatin Zamfara

Gawurtaccen dan bindiga Bello Turji na neman afuwa da sulhu da gwamnati, kwanaki kadan bayan da sojoji suka halaka uban gidansa. Bello ya kuma nemi

Gawurtaccen dan bindiga Bello Turji na neman afuwa da sulhu da gwamnati, kwanaki kadan bayan da sojoji suka halaka uban gidansa.

Bello ya kuma nemi gwamnatin Zamfara ta sanya shi cikin kokarinta na samar da zaman lafiya a jihar.

Turji ya sanar da haka ne a wani bidiyo da ya yi bayan sojoji sun kashe Halilu Sububu.

A baya-bayan nan jami’an tsaro sun hallaka manyan jagororin ’yan bindiga a Zamfara.

Haka ta faru ne musamman bayan tsohon gwamna jihar kuma Karamin Ministan Tsaro, Muhammad Bello Matawalle da manyan kwamandojin soji sun tare a can da nufin ganin bayan ayyukan ’yan fashin daji.

A jihohin Kaduna da Katsina da Neja ma wasu gawurtattun ’yan bindiga sun gamu da ƙarar kwana a lokuta daban-daban a baya-bayan nan.

A cikin bidiyon Turji na ta’aziyyar Halilu Sububu, an ji shi yana cewa ragargazar da sojoji suka yi ba za ta sa su saduda ba.

Amma sai ya ƙara da neman afuwa da sulhu inda ya nemi gwamnatin ta zo su zauna su tattauna a fahimci juna, wanda a cewarsa, hakan zai samar da zaman lafiya a Zamfara da ma ƙasa baki ɗaya.

Kazalika rikici tsakanin ƙungiyoyin ’yan fashin daji ya yi sanadiyyar mutuwar wasu manya daga cikinsu tare da yaransu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments