Pezeshkian : An Mayar Da Martanin Da Ya Dace Ga Isra’ila Domin Kare Iran Da Al’ummarta

Shugaban kasar Iran, Masoud Pezeshkian, ya bayyana cewa an mayar da martani mai mahimmanci ga cin zarafi na gwamnatin Sahayoniyya,” wanda ya hari sansanonin soji

Shugaban kasar Iran, Masoud Pezeshkian, ya bayyana cewa an mayar da martani mai mahimmanci ga cin zarafi na gwamnatin Sahayoniyya,” wanda ya hari sansanonin soji uku da ke kusa da Tel Aviv.

“A bisa la’akari da hakkin tabbatar da zaman lafiya da tsaro ga Iran da yankin, an mayar da martani ga zaluncin gwamnatin Sahayoniyya,” in ji Pezeshkian a kan shafinsa na X.

“An gudanar da wannan aikin ne domin kare muradun Iran da ‘yan kasar.

Firayim Ministan Isra’ila Netanyahu ya sani cewa Iran ba ta son yaki, amma zata yi tsayin daka kan duk wata barazana, inji Pezeshkian.

‘’Wannan kadan ne kawai na karfinmu, kuma Kada ku shiga rikici da Iran.”

Iran dai ta sanar da cewa ta harba makamai masu linzami 200 zuwa Isra’ila a cikin daren jiya Talata, kuma a cewar rundunar kare juyin juya halin Musulinci ta Iran kasha 90 cikin dari sun kai inda ake so.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments