Sayyed al-Houthi: Yemen na samun ci gaba wajen samar da kayan yaki na zamani

Sayyed Abdul-Malik al-Houthi jagoran kungiyar Ansar Allah a kasar Yemen ya bayyana cewa, kasar ta samu gagarumin ci gaba ta fuskar karfin soji a cikin

Sayyed Abdul-Malik al-Houthi jagoran kungiyar Ansar Allah a kasar Yemen ya bayyana cewa, kasar ta samu gagarumin ci gaba ta fuskar karfin soji a cikin shekarun baya-bayan nan.

Sayyid Al-Houthi ya bayyana cewa, juyin da aka samu a kasar Yemen wani mataki ne na ci gaban al’ummar kasar Yemen, inda ya kara da cewa duk wani mataki da matsayar da aka dauka a cikin tsarin wannan juyi na al’umma ne zalla, ba tare da wani tasiri na waje ko tsoma bakin kasashen ketare ba.

Ya bayyana cewa, cikin shekaru 10 da suka gabata, kuma duk da matsalolin da aka haifar ma al’ummar al’ummar Yemen amma sun kiyaye wannan nasarar, tare da fuskantar kalubale da dama, tare da cimma manyan nasarori.

Sannan Sayyed al-Houthi ya jaddada cewa, Amurka da “Isra’ila” da ‘yan korensu a yankin su ne suka fi kowa asara, domin kuwa sun rasa iko da kasar Yemen.

Sayyed al-Houthi Ya zargi Amurka da “Isra’ila” da kawayensu da kai wa kasar Yaman hare-haren wuce gona da iri a tsawon wadannan shekaru da suka gabata, tare da aikata laifukan da suka aikata munana, tare da kakaba wa al’ummar kasar Yamen takunkumi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments