Sojojin Iran Sun Gudanar Da Gagarumin Fareti Da Baje Kolin Makamai A Kasar

Sojojin Iran sun gudanar da wani gagarumin fareti tare da nuna sabbin makamai masu linzami da aka kera a kasar Larduna daban-daban na Iran sun

Sojojin Iran sun gudanar da wani gagarumin fareti tare da nuna sabbin makamai masu linzami da aka kera a kasar

Larduna daban-daban na Iran sun gudanar da faretin soji a daidai lokacin da aka fara gudanar da makon tsaro na alfarma, inda aka bayyana nasarorin da sojoji suka samu na baya-bayan nan da suka hada da kera sabon jirgin sama maras matuki ciki mai cin zango dari da talatin da shida da makami mai linzami mai suna “Jihad”.

Baya ga baje kolin sabbin kayayyaki soji, Iran ta kuma baje kolin makaman kariya da makamai masu linzami a daidai lokacin da aka fara gudanar da bakin makon tsaro (na tunawa da yakin da aka kakabawa Iran), inda Iran din ta aike da sakon gargadi ga makiya kan kuskuren kaddamar da duk wani harin wuce gona da iri kan kasarta.

Manyan jami’an sojin kasar Iran tare da dukkan sassansu ne suka gabatar da jawabai a babban birnin kasar Tehran, da kuma gabar ruwan tekun Fasha da ke yankin Bandar Abbas a shiyar kudancin kasar, da kuma cibiyoyin larduna daban-daban, a gaban Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian da manyan kwamandojin sojoji da dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments