An Bude Taron Hadin Kai Karo Na 38 A Nan Birnin Tehran

A yau Alhamis ne aka bude taron makon hadin a tsakanin musulmi sunna da shi’a a karo na 38 domin raya Mauludin manzon Allah (

A yau Alhamis ne aka bude taron makon hadin a tsakanin musulmi sunna da shi’a a karo na 38 domin raya Mauludin manzon Allah ( s.a.w).

Shugaban kasar Iran Mas’ud Fizishkiyan wanda ya gabatar da jawabi akan  muhimmancin hadin kai a tsakanin al’ummar musulmi sunna da shi’a.

Shi kuwa sakataren kungiyar hadin kai a tsakanin al’ummar musulmi Hamid Shahriari, ya bude taron da jawabi da shi ne karo na 38.

Da akwai baki na cikin gida da kasashen waje da su ka kai 150 da suke halartar taron wanda za a dauki kwanaki uku a jere ana yi.

A kowace shekara ana gabatar da taron makon hadin kai a tsakanin al’ummar musulmi wanda ya samo asali daga wanda ya assasa juyin musulunci na Iran marigayi Ayatullahi Imam Khumaini.

An dauki shekaru 38 ana yin wannan  irin taron inda ake gayyato masana na cikin gida da waje domin tattauna hanyoyin hada kan al’ummar musulmi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments