Araghchi : Ba Ma Jiran Amurka Domin Tattaunawa  

Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya ce Tehran za ta fara tuntubar kasashen Turai don fara shawarwari, ba za ta jira shawarwari da Amurka

Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya ce Tehran za ta fara tuntubar kasashen Turai don fara shawarwari, ba za ta jira shawarwari da Amurka ba.

“Ba za mu amince da wata yarjejeniya ba har sai an tabbatar da muradun mu,” in ji Araghchi a wata hira da aka yi da shi ranar Lahadi.

Araghchi ya ce a baya Turawa sun kakabawa Iran takunkumi iri-iri kan shirinta na nukiliya na zaman lafiya.

“A bayyane yake cewa takunkumin ya gaza,” in ji shi.

A wani bangare na jawabin nasa, Araghchi ya ce, Turawa sun damu da cewa Iran na fitar da nagartattun makamai zuwa kasar Rasha domin yin amfani da su a yakin Ukraine.

“Idan Turai ta damu da gaske, hanyar ita ce tattaunawa ta hakika,” in ji shi.

Kada Turawa su yi tsammanin za a warware damuwarsu ta wani bangare kawai. Iran a shirye take ta tattauna da su, in ji ministan harkokin wajen kasar.

Kalaman na ministan harkokin wajen na Iran sun zo ne bayan ministocin harkokin wajen Birtaniya, Faransa da Jamus – da aka fi sani da E3 – sukayi yi Allah wadai da abin da suke zargin ” Iran da fitar makamai masu linzami zuws Rasha.”

A ranar Talata ma’aikatar kudi ta Amurka da ma’aikatar harkokin wajen Amurka sun kakaba takunkumi kan mutane 10 da hukumomi tara da ke Iran da Rasha, Ciki har da jiragen ruwa da ke kai kaya akai-akai a tekun Caspian tsakanin Iran da Rasha.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments