Shugaban Kasar Comoros Ya Tsallake Rijiya Ta Baya Daga Yunkurin Kisan Gilla

Gwamnatin Comoros ta sanar da yunkurin aiwatar da kisan gilla kan shugaban kasar Gwamnatin kasar Comoros ta sanar da cewa: Wani jami’in tsaron rundunar tsaron

Gwamnatin Comoros ta sanar da yunkurin aiwatar da kisan gilla kan shugaban kasar

Gwamnatin kasar Comoros ta sanar da cewa: Wani jami’in tsaron rundunar tsaron kasar ta Jandarma ya yi yunkuri aiwatar da kisan gilla kan shugaban kasar Ghazali Othmani, amma yunkurin nasa bai kai ga nasara ba kuma a halin yanzu haka shugaban na cikin koshin lafiya babu wani hadari da yake fuskanta.

Kakakin gwamnatin kasar Fatima Ahmadah ta ce, “An kai wa shugaban kasar hari ne a yankin Suleiman-Estandra, yankin da ke kusa da Moroni” a tsaunukan babban birnin kasar. Ta kuma ce, Alhamdulillahi ransa ba ya cikin hadari.

Wata majiya da ke kusa da fadar shugaban kasar da ta bukaci a sakaye sunanta, ta habarta cewa: Shugaban kasar ya samu dan rauni ne da wuka a yayin bikin jana’iza, tare da bayyana cewa, rauninsa ba shi da tsanani, kuma an kama maharan biyu. Wasu majiyoyi biyu na kusa da fadar shugaban kasa sun tabbatar da cewa raunin Othmani kadan ne.

A watan Agustan da ya gabata, Othmani ya bai wa dansa Nour al-Fath sabbin madafun iko, wanda ya ba shi damar tsoma baki a kowane mataki na yanke shawara akasar, wannan na zuwane kasa da wata guda bayan da aka nada shi a matsayin jami’i da ke da alhakin daidaita al’amuran gwamnati, wanda ‘yan adawar ke ganin hakan a matsayin share fage ga dan shugaban kasa na gadon mahaifinsa idan wa’adin mulkinsa ya kare a shekara ta 2029.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments