Hamas Ta Yi Gargadi Kan Tsokanar Da Isra’ila Ke Yi A Masallacin Kudus

Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta yi wani kakkausan gargadi, inda ta yi Allah wadai da tsokanar da Isra’ila ke yi a Masallacin Kudus a

Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta yi wani kakkausan gargadi, inda ta yi Allah wadai da tsokanar da Isra’ila ke yi a Masallacin Kudus a baya-bayan nan, tare da ayyana hakan a matsayin wani abu mai hatsarin gaske.

A baya-bayan nan ne wata kungiyar masu tsattsauran ra’ayin Isra’ila mai suna Temple Mount Faithful, ta fitar da wani bidiyo da ke nuna yadda wata gobara ta kama ta cinye Masallacin Kudus da Dome of the Rock, tare da taken, “Zuwa nan ba da jimawa ba a cikin wadannan kwanaki.”

Kungiyar da ta shahara da kiran rusa Al-Aqsa tare da maye gurbinsa da wajen ibada na Yahudawa, ta fuskanci fushi saboda sakin bidiyon.

Kungiyar Hamas ta yi Allah-wadai da bidiyon, wanda ta danganta  da wani yunkuri na tunzura jama’a da kungiyoyin masu tsatsaurin ra’ayi na Isra’ila ke ci gaba da yi, a karkashin kariyar gwamnatin Isra’ila.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments