Kissoshin Rayuwa: Sirar Fatimah Azzahra(s) 39

39-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka

39-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin alkur’aini mai girma, ko cikin wasu littafan wadanda suka hada da lattafin Dastane Rastan na Shahid Ayatullahi Murtdha Muttahari, ko kuma cikin littafin Mathnawai na maulana Jalaluddin Rumi. Ko kuma cikin wasu littafan da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu a cikin shirimmu na yau.

////…. Madallah, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata, a kuma cikin sirar Fatimah Azzahra(s) diyar manzon Allah(s) sannan mahaifiyar Alhassan da Alhusain (a) da muke mawo muku, mun tsaya a idan muka fara Magana dangane da wafatin manzon Allah(s)  da kuma yadda ya fadawa iyalan gidansa musamman Fatimah (s) musibun da zasu fada masu bayan wafatinsa. Ya kuma fada mata dalla dalla abuwan da zasu faru da ita kamar yadda muka kawo a cikin hadisin Ibn Abbas.

Kuma mun bayyana cewa hadisan da suka zo dangane da abubuwan da zasu faru da iyalan gidan manzon Allah(s) a bayansa suna da yawa, amma a cikin rashin lafiyarsa ta karshe wanda ya rasu a cikinta ya hadasu gaba daya wato Aliyu, da Fatima da Alhassan da kuma Alhussain(a), kafin wafatinsa da sa’o’i a ranar litinin 28 ga watan Safar shekara ta 11 bayan hijira.

Kamar yadda aka ruwaito daga Jabir dan Abdullahil Ansari yana cewa: Manzon Allah(s)  ya fadawa Fatimah (s) a cikin rashin lafiyan da ya rasu a cikinta: Yace: Iyaye na fansarki ki aika a kira mani mijinki.

Sai Fatima(s) ta aika daya daga cikin yayata Alhassan ko Alhussain(a): Ka je ka fadawa babanka ka ce masa: Kakana yana kiranka. Sai Alhussain (a) ya je ya kirashi.

Sai Aliyu (a) ya zo ya shiga wajen manzon All..(s) a lokacin Fatimah tana wajensa tana cewa, kaiton bakin ciki na don bakin cikinka ya baba na! Sai manzon Allah(s)  yace mata: Daga yau babu bakin ciki ga babanki, Ya Fatimah!, amma ka ce kamar yadda babanki ya fada bayan wafatin Ibrahim.  Yace: Idanu suna zubar da hawaye, mai yuwa zuciya ta ji zafi, amma ba zamu fadi abinda zai fusata Ubangiji ba. Kuma lalle muna bakin ciki da rabuwa da kai ya Ibrahim.

Ga wadanda basu sani ba, manzon All..(s) yana da da wanda ake kira Ibrahim, mahaifiyarsa itace Mariya Alkibdiyya. Ibrahim (a) ya rasu a shekara ta 9 bayan hijira yana dan shekara 1 da watannin 6 a duniya, ko watanni 18. Manzon All..(s) yayi bakin ciki da rasuwarsa, shi ne yakewa Fatima (a) nisiha, kan cewa idan shi ma ya rasu to kada ta fadi wani abu fiye da abinda shi babanta ya fada a lokacinda dansa Ibrahim (a) ya rasu.

A wani hadisin manzon Allah(s), a lokacin rasuwarsa ya kira Aliyu, Fatima, Alhassan da Alhussain (a) sannan ya fadawa sauran wadanda suke cikin dakin da su fita.

Sannan ya fadawa matarsa Ummu Salman (r): Ki tsaya a kofar dakin, kada ki bar kowa ya zo kusa. Sannan ya fadawa Aliyu: Zo kusa da ni, sai ya kama hannun Fatima ya sa ta a kan kirjin na wani lokaci, sannan ya kuma hannun Aliyu da dayar hannunsa ya sa a kirjinsa. A lokacinda yake son yayi magana sai ya kasa maganar saboda kuka ta rinjaye shi, a nan sai Fatima da Aliyu da Alhassan da alhussain suka yi ta kuka mai tsanani sabo kukansa.

Sai Fatimah ta ce: Ya manzon Allah(s) ka karya zuciyata, ka kona hantata saboda kokanka, ya shugaban annabawa na farkonsu da na karshenu, ya amintaccen Ubangijinsa kuma manzunsa, kuma ya masoyinsa kuma annabinsa.

Wa zai kula da yayana bayanka? Wa zai kula da kaskancin da zai sameni bayanka, wa zai kula da Aliyu dan’uwanka mataimakin addini? Wa zai kula da wahayin Allah Ta’alah da al-amarinsa? Sannan tayi kuka, ta yi kuka a kan fuskansa sai ya sumbanci kanta, sai Aliyu da Alhassan da Alhussain(a) gaba daya suka zo kusa da kansa suna kuka, sai ya daga kansa, hannun Fatima na hannunsa, sai ya sata a hannunn Aliyu (a), sai ya ce masa: Ya baban Alhassan, ajiyar Allah Ta’ala a ajiyar manzonsa Muhammad(s) na hannunka, ka kiyayewa Allah ka kiyaye mani a cikin al-amarinta, Kuma lallai zaka aikata.

Ya Aliyu! Wallahi wannan itace shugaban matan Aljanna na farako da na karshe, na rantse da Allah wannan itace Maryam Babba. Kuma na rantse da Allah raina bai kai matsayin da ya kai a halin yanzu ba, sai da na roki Allah dangane da su da ku, kuma ya bani abinda na roka.

Ya Aliyu! Ka aiwatar da abinda Fatimah ta umurceka da shi, hakika na umuceta da wasu al-amura wadanda Jibirilu ya ce aikatasu.

Ya Aliyu! Kasan cewa, Lalle ni na yarda da duk wanda diyata Fatima ta yarda da shi.  Haka kuma Ubangiji na da Mala’iku duk sun yarda da shi. Ya Aliyu! Azaba ta tabbata ga wanda ya zalunceta, kuma azaba ta tabbata ga wanda ya kwace mata hakkinta, azaba ta tabbata ga wanda ya keta huruminta… Sannan ra rungumeta ya sumbanci kanta, sai yace: Babanki fansarki ya Fatimah… har zuwa karshen hadisin.

An karbo hadisi daga Imam Sadik(a) … a cikin wani dogon hadisi yana cewa, manzon All..(s) yana fadawa diyarsa Fatima (s): Shin baki yarda ba, ki ga mala’iku daga sassa daban daban na sama suna kallonki su na jirin abinda zaki umurcesu da shi.

Sannan suna kallon mijinki, a dai dai lokacinda halittu gaba daya suka hadu, yana karar wadanda suka zalunceshi a gaban Allah.? Me kike ganin Allah zai yi da wadanda suka kashe yayanki, suka kashe ki suka kashe mijinki…. har zuwa karshen hadisin.

A cikin wadan nan hadisan manzon Allah(s) ya na fadawa diyarsa Fatimah(s) a fili, kan cewa, za’a kasheta a kuma kashe mijinta da yayanta, kamar yadda zamu gani a cikin shirimmu na gaba.

An karbo hadisi daga Imam Musa Al-Kazim (s) daga babansa Imam Ja’afar Assadik(a) ya ce: ya ce babana Imam Sadik(a), shin ba Amirilmuminina ne marubucin wasiyan ba?, manzon All..(s) yana fada masa shi kuma yana rubutawa? Sannan Jabirilu da mala’iku da mala’iku makusanta (a) suna shaida?.

Ya ce: Sai Babana ya sunkuyar da kansa na lokaci mai tsawo, sannan ya daga kansa, sannan yace: Ya baban Alhassan, Abinda ka fada haka ne, amma a lokacinda wafati ya zowa manzon Allah(s), a lokacin ne wasiyya daga Allah ta gasket a sauko, a matsayin littafi ta sauka. Mala’ika Jibirilu ya sauko da shi tare da amintattun Allah daga cikin mala’iku.

Sai Mala’ika Jibirilu yace: Ya Mohammad! Ka bada umurni wa wadanda suke tare da kai su fita sai wasiyyinka, don ya karbeta a wajemmu, sannan mu zama shaida kan cewa ya karbeta daga wajeka, yana mai lamunin zai kiyayeta, wato Ali (a).

Sai manzon All..(s) ya bada umurni ga duk wadanda suke cikin dakin su fice sai Aliyu (a). Sannan Fatimah ta na tsakanin labule da kofa.

Sai Jibirilu ya ce: Ya Mohammadu! Ubangijinka yana sallama a gareka, kuma yana cewa: Wannan shi ne littafin abinda na yi alkawali da kai, na kuma shardanta maka, na riki shaidu daga wajenka kuma na sanya mala’iku su zama shaida, kuma ni na isa shaida ya Muhammad!

Sai Imam Sadik (a) ya ce: Sai gabban manzon Allah(s)  gaba daya suka karkarwa. To masu sauraro saboda kurewar lokaci a nan zamu dasa aya a cikin shirimmu na yau, sai kuma wata fitowa da yardar Allah zamu dora daga inda muka tsaya. Wassalamu alikum wa rahamatullahi wa barakatuhu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments