Iran Tace Kungiyar BRICS Tana Iya Samarta Sabon Tsaron Tsaro A Duniya

Babban sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran Ali Akbar Ahmadiyyan ya bayyana cewa kungiyar tattalin arziki ta BRICS kamar yadda take taka rawa a

Babban sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran Ali Akbar Ahmadiyyan ya bayyana cewa kungiyar tattalin arziki ta BRICS kamar yadda take taka rawa a gina sabon tsarin tattalin arziki a duniya zata iya samarda sabon tsarin tsaro a duniya wanda zai gamsar da kowa nan gaba.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Ahmadiyyan yana fadar haka a yau Laraba a taron tsaro na kasashen BRICS a birnin St. Petersburg na kasar Rasha.

Ya kuma kara da cewa kamar yadda kungiyar Brics ta ke kokarin kyautata harkokin tattalin arzikin kasashen kungiyar a dai dai lokacinda duniya take sauyawa, tana iya samar da wata hukuma mai kula da harkokin tsaro na kasashen kungiyar da kuma duniya gaba daya.

Jami’in ya kara da cewa hukumar tsaro karkashin kungiyar Brics tana iya zama hukumar mai amfani a bangaren yaki da aikata laifuffuka da kuma magancesu. Kama daga barazanar ayyukan ta’addanci, yaki da safarar miyakun kwayoyi ko yaki da laifuffukan yanar gizo da sauransu.

Daga karshe Ahmadiyyan ya kammala da cewa kungiyar BRICS a dai dai lokacinda take magance matsalolin tattalin arziki na kasashen kungiyar zata iya samar da sabon tsarin tsaro a duniya wanda zai maye gurbin na yanzu wanda yake fama da matsaloli.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments