An Sauyawa Kungiyar Yan Ta’adda Ta ‘Komala’ Ta Kurdawan Iran Yan A Ware Wuri A Kasar Iraki

Gwamnatin Iraki ta sauyawa kungiyar yan a ware kurdawan kasar Iran wacce ake kira Komala wuri daga arewa maso gabancin kasar Iraki zuwa wani wuri.

Gwamnatin Iraki ta sauyawa kungiyar yan a ware kurdawan kasar Iran wacce ake kira Komala wuri daga arewa maso gabancin kasar Iraki zuwa wani wuri.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran na cewa, bisa yarjeniyar tsaro wacce aka cimma tskanin kasashen Iran da Iraki a ranar 19 ga watan Maris na wannan shekarar, dole ne gwamnatyin Iraki ta sauyawa yan a waren Komala wuri saboda tabbatar da tsaron kasar Iran daga yammacin kasar.

Majiyar ta kara da cewa a cikin yan kwanakin da suka gabata ne jami’an tsaron yankin Kurdawan kasar Iraki suka shiga sansanin kungiyar yan ta’addar ta Komala inda suka kwacesu suka tafi da su wani wuri daban.

Yan a waren kurdawan Iran na kungiyar Komala dai suna yakar JMI tun bayan nasarar juyin juya halin musulunci a kasar a shekara 1979, kuma sun sha kashe jami’an tsaro da jami’an gwamnatinn Iran a hare haren da suke kaiwa cikinn kasar daga kasar Iraki.

A shekara ta 2022 dakarun IRGN na kasar Iran sun yi luguden wutan kan sansanonin dakarun na Komala. Saboda ayyukan ta’addancin da suke yi a arewa maso gabacin kasar ta Iran. Banda haka kasashen Amurka da HKI suna amfani da yayan wannan kungiyar don cimma wasu manufofinsu a cikin kasar Iran.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments