Isra’ila Tana Karbar Dala 14,000 Akan Kowace Motar Kayan Agaji Da Aka Shigar Yankin Gaza

Manajan kungiyar Agaji ta “Um Ali” dake Kasar Jordan,Samir Balqar, ya bayyana cewa; HKI tana karbar kudade da su ka kai Dalar Amurka 14,000 akan

Manajan kungiyar Agaji ta “Um Ali” dake Kasar Jordan,Samir Balqar, ya bayyana cewa; HKI tana karbar kudade da su ka kai Dalar Amurka 14,000 akan kowace babbar mota ta kayan agaji da ake shigar da ita cikin yankin Gaza.

Jami’in Agajin ya ce, wannan takurawar da HKI take yi, yana kara tsananta shigar da kayan agaji zuwa cikin zirin Gaza da mutanen da suke da matukar batuwa da taimako.

Sai dai ya ce, kungiyar tasu ta kulla yarjejeniya da wata kungiyar Agaji a cikin Gaza domin kaucewa wannan irin takurawar da ake yi musu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted