Da dama daga cikin tawagogin da suke halartar taron babban zauren MDD na shekara-shekara sun fice a yayin da Fira ministan HKI ya fara jawabi, domin nuna kin amincewa da kisan kiyashin yankin Gaza.
A jawabin nasa wanda tsirarun mutane su ka saurare shi, ya soki kasashen Faransa, Birtaniya, Australia da Canada da su ka bayyana amincewarsu da kasar Falasdinu.
Wani kwamiti da MDD ta kafa na bincike akan abinda yake faruwa a Gaza, ya tabbatar da cewa sojojin Isra’ila” suna aikata laifukan yaki cikin ganganci.
HKI tana kara yin bakin jini a tsakanin kasashen duniya saboda yakin Gaza da kuma yadda ta ke take dokokin kasa da kasa.