Guterres: Shirin Gwamantin Mamayar Isra’ila Kan Gaza Wani Babban Hatsari Ne

Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya ya yi gargadi kan mummunan sakamakon Shirin Isra’ila na fadada ayyukanta a birnin Gaza Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya António

Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya ya yi gargadi kan mummunan sakamakon Shirin Isra’ila na fadada ayyukanta a birnin Gaza

Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya António Guterres ya yi gargadi kan mummunan sakamakon matakin da haramtacciyar kasar Isra’ila zata dauka na fadada ayyukan soji a birnin Gaza, yana mai yin Allah wadai da manufofin fadada gine-ginen matsugunan yahudawa ‘yan mamaya a yankunan gabar yammacin kogin Jordan.

A jawabin da ya yi wa manema labarai a jiya Alhamis, gabanin taron kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya a hedkwatar Majalisar dake birnin New York, Guterres ya bayyana cewa, matakin farko da gwamnatin mamayar Isra’ila ta dauka na kwace birnin Gaza ya sanar da wani sabon yanayi mai hadari.

Ya kara da cewa “fadada ayyukan soji a birnin Gaza zai haifar da mummunan sakamako.”

Guterres ya yi bayanin cewa hakan “zai tilastawa dubun dubatar fararen hula da suka gaji sake wani sabon gudun hijira, tare da jefa iyalai cikin hadari.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted