Ƙawancen AES da ya kunshe kasashen Nijar da Mali da Burkina Faso ya kaddamar da bankin raya kasashen 3 na BIDC dauke da jarin CFA biliyan 500 da nufin habaka tattalin arziki da ci gaban kasashen wadanda dukkaninsu sojoji ke mulki.
A karshen makon da ya gabata ne ministocin kudi da tattalin arziƙin kasashen 3 suka hallara a birnin Bamako tare da sanya hannu kan yarjejeniyar kaddamar da bankin, wanda zai habaka tattalin arziki da noma da sauran muhimman bangarori da suka shafi kasashen 3.
Ƙulla wannan yarjejeniya na nufin cimma wata matsaya ta ci gaba tsakanin wadannan kasashen da ke da jerin yarjeniyoyi a tsakaninsu , da ya hada da tsaro tattalin arziƙi da kuma taimakekeniya da kuma musayar bayanai.
Da taimakon bankunan zuba jari na kasashen 3 ne aka samar da wannan gagarumar nasara ta kaddamar da bankin na raya kasashen 3, bayan shafe watanni 7 ana shirye-shirye, inda bayanai ke cewa nan gaba kadan bankin zai fara aiki gadan-gadan.