​UAE Da Isra’ila Sun Janye Takardun Izinin Shiga A Tsakaninsu

2021-01-18 09:13:21
​UAE Da Isra’ila Sun Janye Takardun Izinin Shiga A Tsakaninsu

Ministan harkokin wajen gwamnatin yahudawan Isra’ila Gabi Ashkenazi ya bayyana cewa, yarjejeniyar da suka rattaba hannu a kanta tare da gwamnatin hadaddiyar daular larabawa ta janye izinin shiga cikin kasashensu a tsakaninsu ta fara aiki.

Ya ce wannan babban ci gaba ne a ci gaba da kara karfafa alaka tsakanin gwamnatin yahudawan Isra’ila da kuma kasashen hadaddiyar larabawa, Baharain da kuma Morocco, kuma a cewarsa wannan alaka za ta ci gaba da kara bunkasa.

A halin yanzui bisa yarjejeniyar da aka cimma tsakanin gwamnatin yahudawan Isra’ila da kuma UAE, yahudawan Isra’ila za su iya shiga cikin hadaddiyar daular larabawa ba tare da izinin shiga ba, kamar yadda larabawa daga UAE za su iya shiga dukkanin yankunan Falastinawa da yahudawa suka mamaye ba tare da neman takardun izini ba.

Wasu daga cikin kasashen larabawa sun kulla alaka da Isra’ila ne a daidai lokacin da ita kuma take ci gaba da kara fadada shirinta na mamayar yankunan Falastinawa, da kuma yin kisan gilla a kansu, gami keta alfarmar wurare masu tsarki na musulmi.

015

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!