Search
Close this search box.

Babban Sakataren MDD Ya Ce Bai Kamata A Yi Barazana Ga Ma’aikatan Kotun Duniya Ta ICJ Ba

Kakakin babban sakataren MDD Stéphane Dujarric ya bayyana cewa bai kamata a yi barazana ga ma’aikatan kotun duniya ta ICJ wadanda suke aikinsu a gaza

Kakakin babban sakataren MDD Stéphane Dujarric ya bayyana cewa bai kamata a yi barazana ga ma’aikatan kotun duniya ta ICJ wadanda suke aikinsu a gaza ba.

Tashar Talabijin ta Aljazeera ta kasar Qatar ta nakalto Stéphane Dujarric yana fadar haka a lokacinda yake jawabi ga yan jaridu a birnin NewsYork  na kasar Amurka ya kuma kara da cewa ma’aikatan kotun a halin yanzu suna aikinsu na bincike a  zirin gaza, kuma har yanzun basu karasa ayyukansu ba. Don haka bai kamata wani yayi barazana a garesu ba.

Kafin haka dai wasu yan majalisar dattawan Amurka 12 ne suka yi barazanar kakabawa ma’aikatan kotun kasa da kasa ta ICJ dake birnin Hague idan har kotun ta fidda sammashin kama firai ministan HKI Benyamin Natanyahu kan laifuffukan yakin da ya aikata kuma yake ci gaba da aikatawa a gaza.

A wani labarin kuma wata jiradar Amurka ta bayyana cewa wasu yan jam’iyyar Democrate a majalisar dokokin kasar sun gabatar da wani kuduri wanda yake bukatar a dorawa kotun kasa da kasa ta ICJ takunkumi idan har ta fidda sammashin kama Natanyahu a matsayin wanda ake zargi da kissan kare dangi a gaza.

Gwamnatin HKI ta na ci gaba da kissan kiyashi a gaza tun kimanin watanni 7 da suka gabata, sannan ya zuwa yanzu sojojinta sun kashe falasdinawa fiye  dubu 34 sannan wasu dubu 78 sun ji rauni.

Amma duk da haka gwamnatin kasar Amurka tana ci gaba da bawa gwamnatin HKI makamai wadanda take kissan Falasdinawa da su.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments