Search
Close this search box.

Iran Na Daga Cikin Kasashen Yan Kadan A Duniya Wadanda Suke Da Fasahar Jinyar Cututtukan Rashin Daukar Ciki A Wajen Mata

JMI tana daga cikin kasashe kadan a duniya wadanda suke da fasahar jinyar cutar rashin daukar ciki a wajen mata. Kamfanin dillancin labaran IRIB-News  ya

JMI tana daga cikin kasashe kadan a duniya wadanda suke da fasahar jinyar cutar rashin daukar ciki a wajen mata.

Kamfanin dillancin labaran IRIB-News  ya nakalto shugaban kungiyar likitocin masu jiyar cututtukan haihuwa da rashin haihuwa na Iran yana fadar haka a yau Laraba .

Dar Hamid Chubineh ya kara da cewa a ayyukan bincike da kuma bada magunguna ya zuwa yanzu likitocin matsalolin haihuwa sun sami ci gaba mai yawa kuma sun shiga cikin kasashen da suka kora a wannan fannin.

Dr Chubineh ya kara da cewa a halin yanzu dai sun sami nasarar magance matsalolin rashin haihuwa da dama a kasar, kuma har kuma suna samun majinyata daga kasashen makobta da kuma wadanda suke zuwa yawon shakatawa daga kasashen duniya da dama don jinyar rashin daukar ciki.

A halin yanzu dai ana gudanar da taron kungiyar likitocin cuttukan rashin haihuwa karo na 23 a jami’ar Beheshti dake nan birnin Tehran. Kuma taron ya sami halattan wasu likitoci daga kasashen waje.

Daga karshe Dr Chubineh ya bayyana cewa likitocin kasar Iran a wannan bangaren suna da korewar sosai sannan suna ayyukansu da sauki idan an kwatanta da sauran kasashen da suke da wannan fasahar.

Duk tare da matsin lamba da kuma takunkuman tattalin arziki mafi muni wadanda kasashen yamma suka dorawa JMI, amma mutanen kasar musamman matasa suna iya kokarinsu don samun ci gaban kasar a dukkan fannonin ilmi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments