Ministan harkokin wajen kasar Iran Amir Hussain Abdullahiyan ya yabawa kasar Turkiya kan dakatar da huldar kasuwanci da HKI saboda kissan kiyashin da take yi a gaza. Ya kuma kara da cewa wannan makatin zai kara takurawa haramtacciyar kasar.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Abdullahiyan yana fadar haka a lokacin ganawarsa da shugaban kwamitin aikin tare na majalisun dokokin Iran-Turkiyya wanda yake ziyarar aiki a nan Tehran.
Labarin ya kara da cewa Kayhan Turkmenoglu ya isa nan birnin Tehran tare da tawagarsa wacce ta hada da wasu yan majalisun dokokin kasar Turkiya a jiya Talata.
Abdullahiyan ya kara da cewa kasashen turkiyya da Iran kasashe biyu ne masu karfi a yankin wadanda kuma zasu iya taimaka wajen kyautata al-amuran tsaro a yankin.
A nashi bangaren Kayhan Turkmenoglu ya yabawa kasar Iran da irin goyon bayan da take bawa al-ummar Falasdinu musamman a yakin da take fafatawa da sojojin yahudawa a Gaza.
Ya kuma yi allawadai da hare haren da HKI ta kai kan ofishin jakadancin Iran a birnin Damascus na kasar Siriya. Wanda ya kai ga shahadar manya manyan jami’an sojojin kasar.