Kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen ta gargadi HKI kan duk wani harin da zata kaiwa Falasdinawa a garin rafah na zirin Gaza. Ta kuma kara da cewa idan ta kuskura ta yi hakan, to kuwa zata kara tsananta yaki a yankin.
Muhammad Mufatteh shugaban kwamitin ‘al-aksa’ ya bayyana haka ga tashar talabijin ta Almasirah ta kungiyar, ya kuma kara da cewa kasar Yemen ta kara fadada ayyukanta na hana jiragen ruwan HKI da kuma wadanda suke zuwa haramtacciyar kasar wucewa da babul mandab. Kuma wannan shi ne marhala ta 4 na fadada ayyukanta.
Kafin haka dai gwamnatin kasar Amurka ta kafa kawance na kasashen yamma da wasu kawayenta a yankin don hana kasar Yemen cilla makamai kan jiragen ruwan HKI da kuma wadanda suke zuwa can.
Amma kawancen na Amurka ya kasa cimma manufarta na hana kasar Yemen cilla makamai kan jiragen ruwan HKI ko kuma kan jiragen yakin Amurka da na Burtaniya wadanda suke wucewa da mashigar ruwa ta babul mandab.
A ranar litinin da ta gabace gwamnatin HKI, ta fara kaiwa falasdinawa kimina miliyon 1.5 yan gudun hijira a Rafah hare hare. Masana suna ganin sojojin HKI zasu kara kissan kiyashin da basu taba yi ba a cikin Falasdinawa idan sun faraway garin na Rafah da yaki.
Gwamnatin HKI dai tana ganin wai garin Rafah nan ne tungar kungiyar Hamas na karshe, kuma idan ta kaiwa Rafah hari zata sami cikekken nasara a kan kungiyar. Amma masana da dama sun bayyana cewa sojojin HKI ba zasu taba samun nasara a kan kungiyar Hamas ba ko da ta kwace garin Rafah gaba dayansa.