Gwamnatin Kasar Pakistan Ta Bayyana Cewa Amurka Bata Da Hakkin Umurni Ko Hanata Kyautata Dangantaka Da Iran

Ministan harkokin wajen kasar Pakistan ya bayyana cewa kasarsa ba zata bawa gwamnatin Amurka damar ta bada umurni ko ta hana dangantakar kasuwanci tsakanin Iran

Ministan harkokin wajen kasar Pakistan ya bayyana cewa kasarsa ba zata bawa gwamnatin Amurka damar ta bada umurni ko ta hana dangantakar kasuwanci tsakanin Iran da Pakistan ba.

Kamfanin dillancin labaran ISNA na kasar Iran ya nakalto Mohammad Ishak Dor yana fadar haka a jaridar Down ta kasar Pakistan a jiya Talata. Ya kuma kara da cewa ba kasar Amurka ce take yanke shawara kan harkokin kasuwanci tsakanin Pakistan da Iran ba. Musamman a aikin shimfida bututun gas tsakanin kasashen biyu ba. Ya ce Pakisatan ba zata amincewa Amurka ta zama mai bada umurni wa gwamnatin kasar Pakistan ba.

Gwamnatin kasar Pakistan ce take  fayyace al-amuran da suka shafi kasar ba tare da barin wani yayi shishigi cikin su ba. Muhammad Ishak wanda kuma shi ne mataimakin Faraiminiustan kasar ta Pakistan ya bayyana haka ne a lokacinda wani dan jarida ya tamabashi kan aikin shimfida bututun iskar gas wanda zai samar da iskar gas mai sauki daga kasar Iran don amfanin mutanen kasar.

Ya ce Pakistan tana kallon inda amfaninta yake ne kawai, bata jiran umurni daga wata kasa.   A makon da ya gabata ne dai shugaban kasar Iran Sayyid Ibrahim Ra’isi ya kai ziyarar aiki kasar Pakistan inda bangarorin biyu suka sanya hannu a kan yarjeniyoyi da dama. Amma gwamnatin Amurka ta ja kunnen kasar Pakistan kan cewa ta dakatar da duk harkar kasuwanci da kasar Iran don tana karkashin takunkumanta.  

Idan an kamala aikin shimfida bututun gas daga kasar Iran zuwa Pakaistan dai wannan zai sawwaka matsalolin makamashi masu yawa ga mutanen kasar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments