Boren Amurka Ya Nuna Aibin Tsarin Siyasar Kasar

2021-01-10 21:09:55
Boren Amurka Ya Nuna Aibin Tsarin Siyasar Kasar

Tun bayan da magoya bayan shugaba mai barin gado na Amurka Donald Trump, suka kutsa kai cikin ginin majalisar dokokin kasar, manyan kafofin watsa labaran kasa da kasa ke ganin cewa, boren da ya faru a Amurka ya nuna cewa, akwai babban gibi tsakanin masu wadata da matalauta a kasar, lamarin da zai tsananta rashin amincin a tsakaninsu, kana ya nuna aibin tsarin siyasar kasar.

Kafofin yada labaren da suka yi wannan hangen sun hada da jaridar The Washington Post da mujallar Foreign Policy da CNN na Amurka, da jaridar The World ta Jamus, da jaridar The Guardian ta Birtaniya, da jaridar The World ta Faransa, da shafin yanar gizon jaridar ABC ta Spaniya, da kamfanin dillancin labarai na ITAR-TASS na Rasha, da jaridar The Australian.

Jaridar The Washington Post ta Amurka ta wallafa wani rahoto, inda aka bayyana cewa, taron majalisar dokokin kasar wanda zai tabbatar da sakamakon babban zaben ya kasance tamkar wasa, lamarin da zai kawo baraka ga kasar.

Ita kuwa mujallar Foreign Policy ta Amurka cewa ta yi, Amurka ta riga ta shiga yanayin wahalar mika mulkin kasa cikin lumana.

A rahotonta, jaridar The World ta Jamus ta wallafa cewa, ranar da aka yi boren, ta kasance rana mai duhu ga al’ummun kasar, inda ta nuna shakku kan demokuradiyar Amurkar.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!