Wani rahoto wanda kamfanin UKMTO mai kula da zirgazirgan jiragen ruwa a duniya mallakin gwamnatin kasar Burtania ya bada rahoton cewa, zirga zirgin jiragen ruwa a mashighar ruwa ta Hurmuz ya ragu da kimanin kasha 70% idan an kwatanta da kafin yaki.
Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ya nakalto rahoton UKMTO na mako makon dangane da zirga zirgan jiragen ruwa a duniya yana cewa, har yanzun a makon da ya gabata zirga zirgin jiragen ruwa a mashigar ruwa ta Hurmuz yana kasa da kashi70% idan an kwatanta da kafin fara yakin a ranar 28 ga watan Fabrayru.
Hukumar ta UKMTO ya fidda rahotonsa na wannan makon a jiya Jumma’a ya kuma bayyana cewa zirga zirgan jirage a makon da ya gabata 277 ne wanda ya ragu da kimani kashi 70% kafin yakin.
Mashigar ruwa ta Hurmuz dai tana karkashin ikon sojojin kasar Iran tun bayan fara yakin, sannan Amurka ta amince da hakan, a yarjeniyar Islamabad da ta sanyawa hannu a ranar 17 ga watan yuli na wannan shekarar. Amma daga baya ta dawo tana son kauda sojojin Iran daga mashigar da karfi, wanda ta kasa yi.
Jiragen ruwa da suka saba umurnin kasar Iran a mashigar, ko su hadu da nakiyon da Iran ta sanya a hanyarsu ko kuma sojojin kasar su buge shi da makamai. Akwai yan kadan wadanda suke samun wucewa ta barauniyar hanya.